Posts

Showing posts from December, 2013

Tarihin Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa

TARIHIN SHEIK AMINU DAURAWA KANO :-Sunana Aminu Ibrahim bin Muhammad bin Bilal. Mahaifina shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad mai tafsiri, gidan Zakara-Mai- Neman-Suna Fagge. Yana gabatar da tafisiri duk ranar Litinin da Alhamis, a unguwar Fagge, kusa da tsohuwar tashar kuka. Tsawon shekaru arba’in, kuma yana karantar da ilimi a zauren gidansa, bayan kasuwanci da sana’ar dinki, domin dogaro da kai. Sunan mahaifiyata Hajiya Sa’adatu Al- Mustapha, daga unguwar Bachirawa, karamar hukumar Ungogo. An haife ni a ranar 1 ga wata Janairu shekara ta 1969, a cikin garin Kano, a gida mai lamba 32 unguwar kofar Mazugal, a karamar hukumar Dala. Na fara karatun Alqur’ani mai girma tun ina dan karami, kuma na haddace shi a lokacin ina da shekara 14 zuwa 15. Bayan firamare da sakandare, da na yi, na kuma ci gaba da neman ilimi, domin fadada karatun addini, a wajen wadansu manyan mashahuran malamai na Kano: Wasu na Alqur’ani da tafsir, wasu na Alqur’ani zalla, wasu...