HIRAR DA DAN JARIDA YAYIDA MAI GIRMA ALH DR. Umaru Kwairanga SARKIN FULANIN GOMBE A YAMMACIN JIYA LAHADI.
TAMBAYA: Barka da yamma Ranka yadade: 1. Idan ka zama Gwamna; me kake son kayiwa Al Ummar Jihar Gombe musamman masu karamin karfi? 2. Mene ne yasa kayi imani da cewar kaine mutumin da ya dace da matsayin Gwamnan Jihar Gombe a 2019? 3. Mun san cewa ka kasance a matsayin jagoranci a wurare daban-daban; Menene kadauki jagoranci a gareka? Nagode. AMSA: Idan kuma lokacin da na zama Gwamna na Jihar Gombe, zan bada karfi da fifiko wajen ganin Al Ummar Jihar Gombe sun sami yanayi mai kyau wandazaibasu damar gudanar da Ayyuka, Kasuwanci, Sana'ar Hanu cikin kwanciyar Hankali da cigaba mai dorewa. Tare da nuna kulawa ta musamman ga masu karamin karfi, hakazalika zan tabbatar da cewa suna da damar samun horarwa don bunkasa harkokinsu da kuma bunkasa ƙwarewar su, haɓaka don sanya basira da horarwa don yin amfani da kwarewa da tallafi daga gwamnati don tabbatar da amfani da irin waɗannan shirye-shirye da kokarin. AMSA: Na tabbatar nine nafi cancanta nazamo Gwamnan Jihar Gombe a 2019 sa...