WAYE SARKIN FULANIN GOMBE

Fassaran Rubutun Yakubu Bangu Ahmed:
GA WADANDA BASUSAN WAYE
ALH (DR) UMARU KWAIRANGA (SARKIN FULANIN GOMBE).

WAYE ALH (DR) UMARU KWAIRANGA?
Alh (Dr). Umaru Kwairanga 'Dane ga Marigayi Alh Mohammadu Kwairanga wand shine (Sarkin Fulanin GOMBE) na farko bayan rasuwarsane danshi wato Alh (Dr) Umaru Kwairanga ya gaji Sarautar (Sarkin Fulanin Gombe) daga wajenshi Marigayi ALH MUHAMMADU KWAIRANGA shine Mahaifin Alh (Dr) Umaru Kwairanga kuma yakasance Jagora nagari Adali kuma Kwararren Ma'aikacin Gwamnati, kuma Mai Sarautar Gargajiya a karkashin Masarautar Jihar Gombe,

Alh Dr. UMARU KWAIRANGA Sarkin Fulanin Gombe ya kammala karatun shaidar Digirinsa na farko kan bangaren gudanar da harkokin Kasuwanci wato (Bsc in Business Admin) daga Jamiar Maiduguri, yayi karatun gaba da Digiri akan harkar Kudi da Gudanar da Kudade wato Masters Msc in (Finance and Governance) a Jamiar Liverpool mai suna John Moores University a Kasar United Kingdom daga bisani Jamiar Igbinedion dake Jihar Edo tanemishi da yazo ya karbi Daktan Girmamawa wato (Honourary Doctorate DEGREE).

ALH (DR) UMARU KWAIRANGA (Sarkin Fulanin Gombe) ya samu karban shaidun Kwarewar Aiki a wurare da dama daya halarta kamar haka:
1. Fellow chartered institute of stockbrokers {CIS}
2. Fellow Institute of Directors {FID}
3. Certified pension institute of Nigeria {CPIN}
4. Commodity Brokers ASS .OF NIGERIA
ALH DR UMARU KWAIRANGA yasami halartan Makaranti da Kolejin Ilimi da dama wanda suka shafi fannin Kudi da Kasuwanci a gida Najeriya dama Kasashen waje wanda cikinsu harda Makarantar Harvard bussiness new york wanda take kasar Amurka

DAGA CIKIN BAIWA DA KWAREWA DA ALLAH YAMISHI
A yanzu haka Alh (Dr) Umaru Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) yana daya daga cikin Shugabannin wadannan Ma'aikatu da Kamfanoni kamar haka:
1. Finmal Financial Services as  Group Managing Director
2. Ja'iz bank PLC a Matsayin Darabta
3. Chairman AXA Mansard Pensions 
4. Waila microfinance LTD
5. Gombe Microfinance Bank Ltd
6. First Bank of Nigeria Mortgage Bank Ltd
7. KEDCO Kano Electricity Distribution Company
8. Council Memeber of The Nigerian Stock Exchange (NSE)
9. President Certifiied Pension Institute of Nigeria
10. Council Member Institute of Stock Brokers
11. Former Chairman - Ashaka Cement Plc
12. Director Central Securities Clearing System Plc

A lokacin dayake Shugabantar Kamfanin AshakaCem yasamar da Canje canjen Alkhairi da Nasarori sosai wanda suka hada da:
1. Canjawa Kauyuka waje daga inda suke domin sundau shekaru da dama suna fiskantar barazanar tsagewar gini da kuma girgiza sabida kusancin da suke da Kamfani wannan dalilin yasa lokacin da ALLAH yakawo Alh (Dr) Umaru Kwairanga matsayin Babban Shugaban Kamfanin yabada kwangilar gina musu Gidaje, Makaranta, Asubiti da Masallaci kuma ya mallakawa mutanen kauyukan Gidaje.

2. sama da Shekaru 40 dasuka gabata Kamfani AshakaCem PLC baitaba samun cigaban da aka samu lokacin Shugabancin Alh (Dr) Umaru Kwairanga domin yayi tunanin fadada Kamfani da kuma kawo satin Kayan Aikin domin dena amfani da tsoffin Injuna don samun saukin gudanar da Kamfani. wannan Fadada Kamfanin da sabunta kayayyakin aiki da Alh (Dr) Umaru Kwairanga yayisune don bunkasa Kamfani da kuma kara samar da kudaden shiga wa Kamfanin kuma Shugaban Kasar Najeriya na wancan Lokacinne wanda Ministan Kamfanoni da Kasuwanci ya ya wakilceshi domin dasa tubalin Fadada Kamfanin AshakaCem kuma Aikine wanda zaici Biliyoyin Naira.

3. Hakazalika Alh (Dr) Umaru Kwairanga ya kirkiri sayo kayan Aikin don samar da tsayayyiyar wutar Lantarki.

KAUYEN MAIGANGA
Alh (Dr) Umaru Kwairanga ya kirkiri Megawatts 24 na Wutar Lantarki daga Kauyen Maiganga zuwa cikin Kamfanin AshakaCem, wanda ta sanadin wannan kokarin da Alh (Dr) Umaru Kwairanga yayi ana saran Bangarori dayawa na Jihar Gombe zasu wadata da Wutar Lantarki, zaa iya tabbatar da wannan ta hanyar duba labarun Kamfanin dillancin labarai na Daily Trust wanda Gwamnatin Jihar Gombe tana daga cikin wani bangare wannan Aikin.

 Cikin yan kwanakin da suka gabata Alh (Dr) UMARU KWAIRANGA a Matsayinshi na Darabtan Kamfanin sayar da wutar Lantarki wato Kano Electricity Distribution Company KEDCO yasamarwa mutane da dama Aiki dasukakai Mutane 53 yan Asalin Jihar Gombe ta hanyar amfani da damarshi a Matsayinshi na Darabtan Kamfani wanda Ni mai Fassara wannan rubutu ina daga cikin wadanda suka amfana da wannan damar. hakazalika shekaran data gabata yasamar da Ayyuka makamancin wannan a Kamfanin Wutar Lantarki na Kaduna Electricity Distribution Company KAEDCO kuma yan Asalin Jihar Gombe ne wanda shi wanda yayi wannan Rubutu yana daya daga cikin wadanda suka sami Aiki a cikin wancan daukan

Daga Karshe bayan kadan daga cikin irin Nasarorin da Alh (Dr) Umaru Kwairanga daya cikin Dubbai, saide kullum abunda yake bani mamaki da wadansu mutane masu karamin tunani, Mahassada yan Bakin ciki wadanda basu iya amfanar da Al Ummar Jihar Gombe da komai, har Abada Jihar Gombe bazata taba mantawa da irin guduwamar da ALH DR UMARU KWAIRANGA (SARKIN FULANIN GOMBE).

Mungani kuma Munshaida ireiren cigaban da Jiharmu ta Gombe ta samu a lokacin Mulkin His Excellency Alh (Dr) Muhammad Danjuma Goje hakazalika Mungani kuma Munshaida ireiren cigaban da aka samu a lokacin Mulkin His Excellency Alh (DR) IBRAHIM HASSAN DANKWAMBO.

Mu Gombawa munason musakawa Adalin Jagora wanda kullum Gida da Wajen Nigeria yakeda kyakykyawar Shaida, Mutumin da ALLAH yayima baiwar Ilimi, Basira da Fasaha, Mutumin Mutane mai Taimakon Al Umma, muna Addu'a ALLAH yakawo manashi Gidan Gwamnatin Jihar Gombe a Matsayin Gwamna a shekaran 2019 da yardan ALLAH, wannan bakowa bane sai ALH (DR) UMARU KWAIRANGA (Sarkin Fulanin Gombe) domin yautatamar zaton da tallafawar ALLAH zai iya rike wannan Kujerar.
ALLAH MANA JAGORA.

Comments

Popular posts from this blog

List of Kano State Governors

Tarihin Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa

Buhari names Chairmen for Education Ministry Agencies Dr Sadiq Umar Abubakar Included