Da abincin gargajiya Sardauna ya shirya wa Sarauniya liyafa -Sani One Minute
A lokacin da Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu ta ziyarci garin Kaduna tare da maigidanta a shekarar 1956
, abincin gargajiya Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Jihar Arewa na lokacin, Sa Ahmadu Bello ya shirya musu liyafa da shi, maimakon abincin Turawa irin nasu.
Odilan Sardauna a lokacin, Alhaji Sani One Minute shi ne ya bayyana wa Aminiya haka a yayin da take tattaunawa da shi dangane da cikar Najeriya shekara 50 da samun ‘yancin kai.
Alhaji Sani One Minute ya ce, bayan an tashi daga filin sukuwa inda aka shirya wa Sarauniya gagarumar daba, sai aka wuce gidan gwamnati da ke kan hanyar Kawo inda ofishin Firimiya yake nan ne aka shirya abincin da za su ci a wannan ranar, kuma abincin da aka baje ba na Turawa ba ne irin su salad da sauransu. Abinci ne na gargajiya irin su masa da sinasir da fankasau da Tuwo da miya da sauran abincin gargajiya irin na Hausawa. Kuma ba a kan tebur aka shirya abincin ba, kamar yadda Turawa suke yi, an shirya shi ne a kan shimfidu irin yadda ake yi a kasar Hausa.
Ya ci gaba da cewa, bai sani ba ko Sarauniya ta zo da abincinta daga Ingila kamar yadda shugabannin yanzu suke yi, shi dai a saninsa a nan gidan gwamnatin ta kwana da gari ya waye sai ta tafi Kano inda ta ziyarci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi kuma ta shiga cikin gidan sarkin ta gaisa da matansa, daga nan ba ta je ko’ina ba kuma ba ta kaddamar da wani aiki ba, sannan babu wata sarauta da aka ba ta, sai dai an ba ta kyaututtuka iri-iri da suka hada da kayayyakin gargajiya, amma ba ta sanya su ba a lokacin ziyarar tata. Daga nan ta bar Najeriya.
Alhaji Sani One Minute ya ci gaba da cewa, tun makonni biyu kafin Sarauniyar ta zo, garin Kaduna ya canja fuska. Mutanen gari kowa ya tsaftace gidansa da kewaye, kuma ba gwamnati ce ta sanya su ba, sun yi haka ne domin murnar zuwan Sarauniya, haka kuma duk wani Sarki da ke yankin Arewa yana Kaduna domin tarbarta. Makon guda kafin zuwanta Sarakunan suka turo ‘yan tawagarsu tare da dawakansu. Wadanda suke nesa da Kaduna kuma tun makonnin uku suka turo tawagarsu, inda wadansu suka yi sansani a unguwannin da ke bayan garin Kaduna a lokacin, kamar Unguwar sarki da Badarawa, domin a lokacin babu mutane da yawa a wadannan wuraren ,wadansu kuma sun sauka ne a wurin da yanzu ake kira kofar Gamji.
“A ranar da Sarauniya ta sauka a filin jirgin saman Kaduna da yanzu yake cikin gari, babban direban Sardauna, Alhaji Ali Sarkin Mota ne ya dauko ta, inda aka yi amfani da motocin gwamnati kirar Rolls Royce da Chebrolet da Dodge. Sarauniya tare da mijinta sun shiga motar Rolls Royce da Ali Sarkin mota yake tukawa ne da misalin karfe goma na safe, kuma Sardauna ne ya tarbe su. Daga nan sai aka dunguma zuwa gidan Gwamna inda mutanen gari da ‘yan makaranta suka yi jerin gwano a bakin babbar hanyar da ta shiga garin Kaduna suna son ganinta tare da yi mata barka da zuwa. Haka ake tafiya a hankali har zuwa gidan Gwamnan Arewa na wannan lokacin, kuma duk abin da ake yi ina tare da Sardauna domin ni ne odilansa.”In ji Sani One Minute.
Ya kara da cewa, a gidan Gwamna, Sarauniya ta shafe kamar sa’a guda, daga nan ta fita zuwa filin sukuwa da yanzu ake ce wa Dandalin Murtala, inda duk wani basarake da ya isa a Arewa yake wurin tare da ministoci da manyan jami’an gwamnati. Makada da maroka da sauran jama’a da suka hada da ‘yan jam’iyyar adawa ta NEPU, duk sun hallara a wurin domin karrama Sarauniya. Mata ma ba a barsu a baya ba, sun taru da yawa inda suka daura zannuwa masu dauke da hotunan Sarauniya. duk da muhimmancin da wannan ziyara take da shi, ba a bayar da hutu ga ma’aikata ba, an ci gaba da aiki kamar yadda aka saba a wannan ranar.
A filin sukuwar, Sarauniya ta duba faretin ban girma da jami’an tsaro suka yi, kuma sojoji da ’yan sanda da ’yan makaranta sun rika wucewa ta gabanta suna gaisuwa. Daga nan sai Sardauna ya yi jawabi da Turanci da Hausa, ita kuma Sarauniya ta yi nata jawabin da Turanci aka fassara da Hausa. Sannnan Sarakuna suka yi hawan daba. Mawaka irin su Mamman Shata da A’isha Fallatiya daga kasar Sudan suka kara wa bikin armashi da wakokinsu. Sai dai duk shagulgulan da aka yi babu matan ministoci ko na wani babban jami’in gwamnati a wurin, amma akwai manyan jami’an gwamnati mata da suka halarta a matsayinsu na jami’an gwamnati.
Comments
Post a Comment