Yadda gwagwarmayar kafa Najeriya ta kasance
Friday, 01 October 2010 03:57
Tarihi ya nuna cewa mutanen farko da ake jin an fara samu a kasar nan, wadda ita ce kasa mafi yawan jama’a a Nahiyar Afirka, su ne mutanen Nok da ke yankin Karamar Hukumar Jaba ta Jihar Kaduna ta yanzu.
Tarihi ya nuna cewa shekara dubu biyu da suka gabata ’yan kabilar Nok sun yi suna wajen sarrafa karafa suna kera wasu manyan kayayyakin kawa.
Sannan yankunan Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya da Kalaba da ke Kudu maso Kudu ana kyautata zaton su ne tushen kabilar Bantu da suka yi hijira suka bazu zuwa Afirka ta Tsakiya da kasashen Kudancin Nahiyar Afirka shekara dubu daya zuwa dubu biyu kafin haihuwar Annabi Isa.
A Arewacin Najeriya, Katsina ta kafu shekaru da dama kafin haihuwar Annabi Isa (Alaihis Salam), yayin da Kano ta kafu shekara 900 Miladiyya wato bayan haihuwar Annabi Isa (AS) da shekara dubu.
Kodayake Daular Kanem Borno da ta mamaye yankin Tafkin Chadi wadda ta nausa wasu sassa na kasashen Nijar da Kamaru da Chadi ta mamaye Arewacin Najeriya har na tsawon shekara 600, wadannan garuruwa sun kasance cibiyoyin kasuwanci a yankin a tsakanin kabilar Berber na Arewacin Afirka da kuma garuruwan da ke karkashin Daular Kanem Borno.
Ana cikin haka ne, a farkon karni na 19, Shehu Usman Dan Fodiyo ya bayyana inda ya jagoranci jihadin gyara al’umma kuma ya ci yawancin garuruwan Arewacin Najeriya da yaki, ya kafa Daular Musulunci ta Usmaniyya mai cibiya a Sakkwato.
Masarautun Ife da Oyo na kabilar Yarabawa a Kudu maso Yamma kuma sun yi suna a shekarun tsakanin shekara ta 700 zuwa 900 da kuma 1400 Miladiyya wato karni na 15. Bisa ga tarihin Yarabawa, Ile- Ife ita ce tushen bil Adama, a ra’ayinsu. A yankin Ile-Ife ne ake sassake-sassaken terra cotta wanda ya yi suna a wasu manyan kasashen duniya.
Masarautar Oyo ta taba fadada har zuwa cikin kasar Togo, wanda hakan ya nuna irin dadaddiyar mu’amala da zumuntar da ke tsakanin kasashen biyu.
Sannan akwai masu ganin cewa masarautar Benin a Kudu maso Kudu, ita ce wadda ta fi kowace masarauta ko daula girma da karfi a kasar nan a can baya. Masarautar ta yi zamani daga karni na 15 zuwa na 19 wato ta shafe shekara 400 a matsayin daula daya, kuma girmanta ya kai har cikin Eko (Ikko), garin da zuwan Turawan Portugal suka sauya wa suna zuwa Legas.
Ife da Benin sun yi suna ta wajen amfani da hauren giwa da katako da karafa wajen kera abubawan da suke sayarwa.
A bangaren Kudu maso Gabashin Najeriya kuma Daular Nri ta ’yan kabilar Ibo ce ta samu kafuwa a kusan karni na goma har zuwa shekarar 1911, abin da ya sa ta kasance daular da ta fi kowace dadewa a tarihin Najeriya, kuma tana karkashin ko Eze (Sarkin) Nri ne. ’Yan kabilar sun yi ittifakin cewa garin Nri shi ne tushen kabilar Ibo. Garuruwan Nri da Aguleri inda tarihi ya nuna nan ne asalin kabilar Ibo na cikin daular Umeuri sun fito ne daga tsatson Sarkin Eri ne.
Bayan kabilar Ibo, akwai wasu kabilu a yankin Kudu maso Gabas, da a yanzu suke Kudu maso Kudu, wadanda suka hada da Ibibiyo da sauransu. A wannan yankin ne aka samu wasu daga cikin manyan sassake-sassake kamar Igbo-Ukwu da ke da dadadden tarihi a Afirka ta Yamma.
Gabanin shigowar Turawan mulkin mallaka Najeriya, mutanen kasar nan na zaman lafiya da juna tare da yin harkar kasuwanci ba tare da kokawar neman samun arzikin kasa ko mulki ba, a dukkan sassan kasar.Kowane bangare yana amfani da tsarin mulkinsa na asali domin tafiyar da harkokin shugabantar jama’arsa. Wannan ya kawo cigaban yankunan Najeriya.
Kafin samun ’yancin kai
Turawan Potugal su ne suka fara shigowa Najeriya don harkar kasuwanci ta tashar ruwan da suka ba wa suna Lagos da ta Kalaba a karni na 17 zuwa na 19. Turawan sun rika shigo da kayayyakin kasuwanci suna musayarsu da bayi a wancan lokaci, kuma shugabannin al’ummar wuraren ne kadai ke mu’amala da su kuma ke samun riba daga cinikin da ke gudana.
A 1807 ne Birtaniya ta dakatar da cinikin bayin da take yi a Najeriya, kuma bayan yake-yaken rububin mallakar kasashe, Birtaniya ta kafa wata rundunar soja a Afirka ta Yamma a wani yunkuri na dakatar da cinikin bayi da kasashen duniya ke yi.
A shekarun 1884 zuwa 1885 ne, aka gudanar da wani babban taro a kasar Jamus da ake kira Taron Berlin, inda aka kakkasa kasashen Afirka zuwa yankuna daban-daban na mulkin mallakan Turawa. Bayan taron, Birtaniya ta samu yankuna da dama a Yammacin Afirka, kuma Najeriya na daga cikin kason da aka ba ta.
Har zuwa wancan lokacin ikon Turawan mulkin mallakar bai karasa Arewacin Najeriya ba, yawancin ikonsu ya tsaya ne a Kudu da yankin Legas.
A 1903 Turawan sun sami nasarar mamaye Arewa bayan tafka gumurzu tsakaninsu da dakarun sarakunan Daular Usmaniyya, wannan ne ya yi sanadiyyar rasuwar marigayi Sarkin Musulmi Attahiru da faduwar Daular Sakkwato. Turawan mulkin mallakar sun cafke sarakuna kamar Sarkin Kano Alu bayan ya ki mika musu wuya, inda suka kulle shi a Lakwaja. Bayan wannan ne Turawan suka sami mallakar yankunan biyu da yankin Ikko.
Kuma a 1914 ne wakilin Sarauniya Ingila a kasar nan Gwamna Janar Fredrick Lugard ya hade yankunan Kudu da Arewa aka sa wa kasar suna Najeriya.
Yadda Najeriya ta sami sunanta
Sunan Najeriya ya samo asali ne daga kogin Neja inda a ranar 8 ga Janairun 1897, wata ’yar jarida wadda daga baya Fredrick Lugard ya aura, mai suna Dame Flora Louisa Shaw, ta rubuta wata kasida a jaridar The Times ta Ingila, cewa ya kamata a sa wa kasar nan suna Najeriya wato “Niger da Area”, saboda kogin Neja da ya bi ta cikin kasar.
Najeriya na makwabtaka da Jamhuriyyar Benin a Yamma sai Chadi da Kamaru a Gabas da kuma Jamhuriyyar Nijar a Arewa. Kuma baki dayan kasashen da Najeriya ke makwabtaka da su Faransa ce ta mulke su, in ban da Arewacin Kamaru da Birtaniya ta mulka zuwa wani lokaci kafin Faransa ta karba.
Tun daga wancan lokacin Birtaniya ta rika gudanar da mulkin mallaka karkashin tsarin mulkinta wanda ke da Majalisar Dokoki da ta kunshi ’yan kalilan din wakilai daga ’yan Najeriya. Da tafiya ta yi tafiya an nada wasu ’yan Najeriya su shugabanci wasu yankunan kasar.
Wannan ya ba su karin ikon cin gashin kai, sai dai kuma hakan shi ne ummul aba’isin haifar da rikice- rikicen addini da na kabilanci a sassa daban-daban na kasar nan.
Bayan da Turawan suka ga lamarin ya-ki-ci-ya-ki cinyewa, sai suka sake fasalta kasar, inda suka kasa ta zuwa manyan jihohi uku, bisa tsarin kabilanci, kabilar Yarabawa a Yamma, Hausawa da Fulani masu rinjaye da sauran kabilunsu a Arewa, sai kabilar Ibo da sauransu a Gabas. Wannan tsari ne ya raba ’yan kasar bisa turbar kabilanci, kuma kowane bangare ya samu karfin fada-a-ji a yankinsa.
Bayan da wadannan manyan kabilun uku na Najeriya suka samu karfin mulkar jama’arsu, nan da nan sauran kananan kabilun kasar suka fara neman a ba su ’yancinsu inda aka yi ta samun rikici.Domin a sami kwanciyar hankali a 1954, an cimma wata yarjejeniyar rarraba ikon tafiyar da ayyukan cigaban al’umma da cigaban kasa kamar kiwon lafiya da ilimi da sauransu, a tsakanin kabilun kowane yanki. Ita kuma Gwamnatin Tarayya ta dauki kula da harkokin tsaro da tattalin arzikin kasa.
Amma duk da haka wannan mataki bai kawo karshen rikicin ba, sai da aka kafa wata hukuma a 1957, mai suna Willink Minorities Commission, wadda ta duba korafe-korafen kananan kabilu a wancan lokacin.
A 1953, Chief Anthony Enahoro ya gabatar da wani kuduri a Majalisar Dokoki ta kasa yana neman a ba Najeriya ’yancin kai a1957. Sai dai kuma wakilan Arewa a majalisar sun ki amincewa da hakan, saboda karancin kwararrun da za su tafiyar da harkokin mulki a yankin da kuma gudun cewa mutanen Kudu za su mamaye harkokin gwamnati a yankinsu.
Kuma a dan wannan lokacin ne aka yi ta tura ’yan Arewa kasashen Turai, musamman Ingila domin yin kwasa-kwasai ta yadda za su sami ayyuka kamar su akawu da akanta idan suka dawo gida. Kuma domin samun zaman lafiya bisa wadannan bambance-bambance ne aka amince a daga batun karbar mulki ko samun ’yancin kan kasa zuwa 1960 inda za a ba Najeriya ’yancin kai.
Bayan samun ’yancin kai
Bayan shafe shekara da shekaru ’yan kishin kasa suna gwagwarmayar kwato wa kasar nan ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, a karshe hakarsu ta cimma ruwa, inda ranar 1 ga watan Oktoban 1960, yau shekara 50 cif, Sa Abubakar Tafawa Balewa wanda ya zamo Firaministan Najeriya na farko ya karbi tutar ’yancin kasar nan daga hannun Gwamna Janar Sa James Willson Robertson, wanda ya mulki Najeriya daga 1955 zuwa 1960.
An gudanar da zaben farko a Najeriya a 1959, kuma duk da cewa Jam’iyyar NPC ta Arewa ita ce ta fi samun kuri’u a zaben, to amma yawan kuri’un da ta samu ba su isa ta kafa Gwamnatin Tarayya ita kadai ba, abin da ya sa ta kafa gwamnatin hadin gwiwa tare da Jam’iyyar NCNC ta ’yan kabilar Ibo. Kuma bayan da kasar ta sami ’yancin kai a 1960, wadannan jam’iyyu biyu ne suka kafa gwamnati, inda bisa tsari Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya kamata ya zama Firaminista, amma sai ya mara wa mataimakinsa Sa Abubukar Tafawa Balewa baya ya zamo Firaministan farko, shi kuma Dokta Nnamdi Azikiwe ya zama Gwamna Janar na farko dan Najeriya.
A daya bangaren kuma Jam’iyyar Action Group ko AG ta Yarabawa da Cif Obafemi Awolowo ya jagoranta, sai ta kasance jam’iyyar adawa.
Bambance-bambancen addini da al’adu da ke tsakanin Hausawa a Arewa da Ibo a Gabas da kuma Yarabawa a Yamma, sun haifar da rashin yarda da juna inda a karshe aka rika samun rikice-rikice a gwamnatin hadin gwiwar wadanda suka kai ga rarrabuwar kai tsakanin wadanda ke cikinta. Ita ma jam’iyyar adawa ta AG ta sami rarrabuwar kai tsakanin ’ya’yanta, inda a 1962 wani bangaren jam’iyyar ya ware ya kafa sabuwar jam’iyya mai suna Nigerian National Democratic Party (NNDP), wadda Samuel Ladoke Akintola ya jagoranta.
Rigingimun siyasa sun mamaye gwamnatin wancan lokaci, abin da ya kai ga kirkiro Jihar Yamma ta Tsakiya wato (Mid-Western Region) a 1963 daga Jihar Yamma.
Ranar 1 ga Oktoban 1963 ne aka amince da kundin tsarin mulkin kasar kuma Najeriya ta zama wakiliya a Kungiyar Kasashen Rainon Ingila (Commonwealth).Kundin Tsarin Mulkin ya sa Najeriya ta koma mai bin tsarin tarayya da ke da shugaban kasa da mataimakinsa, inda aka zabi Dokta Nnamdi Azikiwe a matsayin shugaban tarayyar Najeriya.
An gudanar da kidayar jama’a a 1963, wanda ya nuna Jihar Arewa ce ta fi kowace jiha daga cikin jihohin nan uku yawan jama’a. Sakamakon kidayar ya jawo rikici tsakanin yankunan kasar nan, inda Jam’iyyar NCNC ke ganin an yi haka ne domin kawai a ba Jihar Arewa kujeru mafi yawa a Majalisar Dokokin Kasa.
Bayan da rigingimun suka ki-ci-suka-ki-cinyewa, sai sojoji suka yi juyin mulkin farko a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966, inda suka halaka Firaministan Najeriya, Alhaji Sa Abubakar Tafawa Balewa da Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da wasu manyan sojoji daga Arewa da Firimiyan Yamma S. L. Akintola da wasu jami’an Gwamnatin Tarayya.
Kasar da a yau ake kira Najeriya hadakar wasu tsofafffin dauloli ne da suka rayu a matsayin kasashe mabambanta masu zaman kansu shekaru aru-aru kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.
Duk da irin dimbin matsalolin da kasar take shiga ta fita, bisa lura da cewa hadakar kasashe ne suka tayar da Najeriya, tilas mu fito mu yi murna, mu yi godiya ga Allah, mu yi shagali da shagulgula ganin cewa mun shafe rabin karni wato shekara hamsin muna zaune a matsayin kasa daya.Tarihi ya nuna cewa mutanen farko da ake jin an fara samu a kasar nan, wadda ita ce kasa mafi yawan jama’a a Nahiyar Afirka, su ne mutanen Nok da ke yankin Karamar Hukumar Jaba ta Jihar Kaduna ta yanzu.

Comments
Post a Comment