MU ‘YAN KUNGIYAR JAMA’ATU IZALATIL BID’AH WA IQAMATIS SUNNAH SAI MU YI MURNA MU YI FARIN CIKI MU GODE ALLAH(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

11/3/1434. H 23/1/2013 M
Lalle mu ‘Yan Kungiyar IZALA sai mu yi murna mu yi farin ciki saboda yadda Allah Madaukakin Sarki yayi wa shugabanninmu mutum goma sha hudun nan da suka rubuta wa Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah wa Iqamatis Sunnah Constitution dinta watau:- M. Isma’ila Idris. M. Hudu Chikaji Zaria. M. Sidi Attahir Sokoto. M. Alhasan Sa’id Adam Jos. M. Sa’idu Hasan Jingir. M. Rabi’u Daura. M. Yakubu Musa Hasan Katsina. A. Ahmadu Gyallesu. A. Yaro Bichi. A. Bashir Makama. A. Ali Ibrahim Hikima. A. Bala Jaban. A.
Mamman Malunfashi. A. Isa Waziri.Sai mu gode wa Allah Madaukakin Sarki da Ya yi wa wadannan mutum 14 muwafaka da taufiiqi a lokacin da suka rubuta Constitution din kungiyar Izala, ta yadda suka rubuta shi bisa tsarin da ya dace, watau suka rubuta shi a bisa tsarin da bai saba wa Shari’ar Musulunci ba. Ta yadda dukkan wani wanda ke son ya maida kungiyar wata kungiyar ‘yan bidi’ah mai take ka’idodin Shari’ah ba zai samu damar yin hakan ba matukar dai zai jingina wannan aikin nasa ne da Constitution dinta watau tsarin
mulkin tafiyar da lamuranta, bai isa ya fada cikin wata bidi’ah ko wata karkata ba sai in ya bar yin aiki dawannan Constitution din nata ya koma can yana hauragiyasa kamar yadda sauran ‘yan bidi’ah da masu
bautar son zuciya ke yi cikin kowane zamani kuma a ko wane guri. Lalle wannan abin farin cikine matuka wanda zai wajabta wa ‘yan wannan kungiya su gode wa Allah Madaukakin Sarki a kan shi.
************************************************************************************
Idan kana son fahimtar gaskiyar wannan magana tawa sai ka lura da wasu abubuwa kamar haka:- Na farko: An rubuta a bangon Constitution din Kungiyar Izala kamar haka:-
{ ﻻ ﻃﺎﻋﺔ ﻟﻤﻦ ﻟﻢ ﻳﻄﻊ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ. ﺣﺪﻳﺚ
ﺷﺮﻳﻒ.{
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﺍﺣﻤﺪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ ١٣٢٤٨، ﻭﺃﺑﻮ ﻳﻌﻠﻰ
ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ ٤٠٤٦، ﻭﺍﻟﺸﺎﺷﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ١٢٦٥،
ﻭﺍﻟﻀﻴﺎﺀ ﺍﻟﻤﻘﺪﺳﻲ ﻓﻲ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﻤﺨﺘﺎﺭﺓ ٢٣٤١ .
ﻭﺣﺴﻦ ﺇﺳﻨﺎﺩﻩ.
Ma’ana: {Babu wata daa’a ga wanda bai yi wa Allah Mai girma da buwaya daa’a ba. Hadithi mai daraja}.
Kun ga a nan da za a samu wani fitsararre wanda son mulkar jama’a ya yi tsatsa cikin zuciyarsa, ko hassada to toye tunaninsa, har hakan ya kai shi ga neman take wasu ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah, kuma yanemi tilasta wa mutane yin masa daa’ah a kan hakan to sai ace da shi: Ba ka da wannan gurbin a cikin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah, saboda ita kungiyar IZALA an ginata ne a kan haramta daa’a da biyayya ga dukkan mutumin da yaki yin biyayya da daa’a ga Allah Madaukakin Sarki da kuma ManzonSa mai tsira da amincin Allah.
*********************************************************************************
Na biyu: An rubuta a SECTION
ONE (b) kamar haka:- ((Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah’ Kungiya ce ta addinin Musulunci wacce Musulmai suka kafa ta, sannan tana da Headquarter watau jigo a Jos babban birnin Jihar Plateau. Ita dai kungiya ce wacce ba ruwanta da duk wata kungiya ta asiri, kokuma wata darika ta kowace iri, haka kuma ba kungiya ce ta wata siyasa ba)). Kun gani a nan idan wani ya nunason zuciya ya zabi yi wa duniya karya, ya nemi yi wa kungiyar IZALA sharri ta hanyar nuna wa duniya cewa ita kungiyace mallakar wani mutum daya tak, domin dama kungiya ce da wani mutum guda ya kafa, to sai a ce da shi karya kake yi azzalumin banza mayaudari, lalle hakika Kungiyar Izala kungiya ce da wasu Musulmi suka hadu suka kafa saboda yakar bidi’a da tsaida sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ta hanyar yin wa’azi da karantar da mutane cikin makarantu, wannan shi ne abin da yake rubuce cikin constitution din Kungiyar wanda mutum 14 sukayi ittafaki a kan rubuta shi, cikinsu kuwa har da M. Isma’ila Idris Bin Zakariyya. Sannan kuma wanda duk Shaidan ya batar bayan wannan ittifaki nasu ya je ya yi wani shaidan karya ba za mu taba karban maganrsa ba wacce yagina a kan son zuciya ko hassada ko son mulki, sannan mu bar bin abin da suka rubuta a hade a lokacin da hammin kowa daga cikinsu shi ne: Tsaida Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah da kuma yakar bidi’un da Shaidan ya cusa cikin addinin Musulunci.
**********************************************************************************
Na uku: An rubuta a SECTION SIX
PART ONE kamar haka: ((JAGORANCIN KUNGIYA: (I)
Jagorancin wannan kungiya ya rataya ne a wuyan shugabannin da wannan kungiya ta ga sun dace su shugabance ta, wanda kuma za su kasance a karkashin shugabancin wani shugaba da ta zaba, don kuwa Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: “Idan Musulmai uku sun hadu dole ne su sanya dayansu shugaba, don tafiyar da al’amarinsu”)). Kun gani a nan Constitution din Kungiyar Izala ya fito fili ya ce: Dukkan shugabannin kungiyar Izala za su kasance ne a karkashin shugabancin shugaban da Kungiyar Izala ta zaba. Saboda
haka, ke nan da za a samu wani mutum wanda son mulki ya gigita masa tunanin shi har ya nemi nada
kansa shugaban kowa a cikin Kumgiyar Izala sai a taka masa Birki sannan a ce da shi: Kungiyar Izala ta rika ta tabbatar da cewa dukkan wanin shugaban wani bangare na Izala: Shugaban majalisar Dattijai ne, ko shugaban Majalisar Iyayen Kungiya ne, ko shugaban Majalisar Aikace-Aikace ne, ko shugaban Majalisar Wa’azi ne, ko shugaban Majalisar Sadarwa ne’ ko shugaban Majalisar Shari’a ne, ko shugaban Majalisar Ilmi da Ilmantarwa ne, ko shugaban Majalisar Kudi ne, ko shugaban Majalisar Bincike ne, ko shugaban ‘Yan’agaji ne, koma shugaban wani bangare ne daga cikin bangarorin kungiyar Izala to shugaban da Kungiyar ta zaba shi ne shugaban shi.
**********************************************************************************
Na hudu: An rubuta a maganar karshe cikin Constitution din Kungiyar IZALA a (iv) CLOSING
REMARKS watau jawabin RUFEWA kamar haka:- {Muna kara tabbatar wa jama’ar Musulmin Duniya cewa, wannan kungiya tamu kungiya ce da aka kafa ta domin ta karantar da jama’ar Musulmi ta hanyan yi
musu wa’azi da kuma kafa makarantu, ita ba kungiya ba ce ta siyasa, ba kuma kungiyar asiri ba ce, haka kuma ba ta darika ba ce ko wace iri, ita dai kungiya ce ta addinin Musulunci tsantsa kamar yadda  Annabinmu Muhammad (S.A.W.) ya taho da shi. Haka kuma ba ruwanta da tilasta ma wani ko wassu zamowa dan ko yan wannan kungiya kamar dai yadda ya riga ya gabata a can sama, wannan kungiya dai ba hukuma ba ce, haka kuma ba ruwanta da shishigi a harkar hukuncin kasan nan ko wata kasa, wanda ta
kasance akwai yan wannan kungiya a cikinta, (manufa dai ita wannan kungiya ba ta da ikon hana hukuma yin hukunci a kan dan wannan kungiya a lokacin da duk aka same shi da wani laifi a cikin kasan nan ko wata kasan). Kuma duk mutumin da ya yi Imani da Alkur’ani da hadithan Annabi Muhammad (SA.W.) da kuma
Ijma’in Malamai na kwarai, to ko a dokan daji yake shi kadai babu shakka dan wannan kungiya ne. Haka kuma matukar yana sauraron wa’azinta babu shakka yin haka ma taimakawa ne. Ita dai wannan kungiya ba da wani kati ko wata shaida na nuna cewa lalle sai ka yi rajista matukar dai ka yi Imani da abin da aka fadi a sama to babu shakka Kai dan wannan kungiya ne. Kuma sannan kowa na da hakkin ba wa kowa shawara, ko nasiha ko mai girman wanda za a yi wa nasihar ko ba da shawarar, ko mai kankantar shi mai nasihar
ko shawaran matukar yin shawarar ko nasihar an yi yadda Musulunci ya shirya abubuwa}. Intaha. Kun gani a nan idan har an samu wasu wadanda Shaidan ya rikitar da tunaninsu har suke ganin cewa IZALA tasu ce ba ta wani ba, ko suke ganin cewa su ne suka riga shiga IZALA saboda haka duk wani wanda ba su ba ba yi da wani hakki a cikinta, to sai a ce da su karya kuke masu bautar son zuciya, da tafiya cikin jahilci da
rudani, Yana rubuce cikin tsarin mulkin Izala cewa: Duk wanda ya yi imani da Alkur’ani da Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ko ma a Ina yake to lalle shi wannan dan IZALA ne. Ke nan ba lafuzan IZALA ba ne abin da yake muhimmi a’a yin aiki da Alkur’ani da kuma ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne muhimmi. Allah Ya taimake mu Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta, Ya nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon kin ta. Ameen.

Comments

Popular posts from this blog

List of Kano State Governors

Tarihin Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa

Buhari names Chairmen for Education Ministry Agencies Dr Sadiq Umar Abubakar Included