History of Alhaji Dr. Ado Bayero

TARIHIN (Margayi Alhaji Dr. Ado Bayero)
An haifi marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero a watan Yuli na shekarar 1930.
Mahaifin sa shi ne Alhaji Abdullahi Bayero wanda yayi sarautar Kano tsawon shekaru 27.
Bayan karatun Kur'ani da ya yi a gida ya yi karatun primary ta gidan sarki da ke kofar Kudu a shekarun 1937, sanna ya halarci makarantar middle school wadda aka fi sani a yanzu da Rumfa College, inda daga nan ya halarci makarantar koyon harshen larafci ta S.A.S wadda ya kammala a 1947.
A shekarar 1947 ne ya fara aiki a bankin Africa na Birtaniya wanda aka fi sani da First Bank a yanzu, sannan ya koma aiki a NA (Native Authority) a 1949 a matsayin magatakarda.
A 1952 kuma ya je karin ilimi a makarantar koyon gudanar da mulki dake Kongo a Zaria.
Bayan dawowar sa Kano ne ya fara aiki a matsayin babban magatakarda a Native Authourity.
An zabi Alhaji Ado Bayero a matsayin dan majalisa mai wakilitar Kano a Majalisar dokoki ta Kaduna a 1954, inda ya zauna har zuwa shekaru uku.
Margayi Sarki da Yarima Charles
A 1957 kuma sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya nada shi wakilin doka, wanda a lokacin ya ke dai dai da babban jami'in tsaro na Kano, har zuwa 1952 lokacin da gwamnatin Nigeria karkashin Firayi minista Sir Abubukar Tafawa Balewa ta nada shi jakadan Nigeria a kasar Senagal.
A ranar Juma'a 11 ga watan Oktobar 1963 ne kuma aka nada Alhaji Ado Bayero a matsayin sarkin Kano bayan rasuwar Sarki Muhammad Inuwa dan Sarkin Abas.
Ya hau sarautar Kano yana da shekaru 33, sannan ya yi mulkin na tsawon shekaru 51.
Alhaji Ado Bayero shi ne sarkin mafi dadewa a sarakunan Fulani a kano da suka fara mulki bayan jihadi a shekara ta 1807.
Marigayin sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya rasu yana da shekaru 84 a duniya, ya kuma bar mata 4 da 'ya 'ya sama da sittin da jikoki fiye da 300.
ALLAH YA JIKAN SA DA RAHAMA YA KYAUTATA TAMU IN TAZO. AMIN.

Comments

Popular posts from this blog

List of Kano State Governors

Tarihin Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa

Buhari names Chairmen for Education Ministry Agencies Dr Sadiq Umar Abubakar Included