CHARTERED INSTITUTE OF STOCKBROKERS (CIS)

A Jiya Ranar Talata (Tuesday) 5/July/2017 Ma'aikatar Saye da Sayarwa na Hannun Jari wato (Charterde Institute of Stockbrokers) ta Gudanar da Taron karawa juna sani akan bunkasa Tattalin Arziki ta hanyar Zuba Hannun Jari (Workshop 2017) domin ganin sunfidda Kasarmu Najeriya a halin datake ciki wanda Alh Dr. Umaru Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) ya Jagoranci gudanar da wannan Taron kuma Taron ya gudanane a Babban dakin Taro na Lagos - Osun Hall dake cikin Babban Masaukin Baki na Kasa da Kasa dake Birnin Tarayya Abuja Nigeria wato Transcorp Hilton Abuja.

Hakazalika Taron yasamin Halartan masana Tattalin Arziki a gida da wajen Najeriya daga cikin mahalartan sunhada da Ministar Kudi ta Tarayyar Najeriya Kemi Adeosun, Gwamnan Babban Bankin Najeriya Central Bank of Nigeria Mr. Godwin I. Emefiele, Shugaban Ma'aikatar Kula da Hadahadar Hannun Jari ta Kasa The Nigerian Stock Exchange (NSE) Mr. Oscar, Shugaban Bankin Musulunci na Farko a Najeriya Jaiz Bank Plc kuma Tsohon Ministan Kudi a Najeria Dr. Umaru Mutallab, Babban Manajan Kamfanin Sadarwa na Airtel Nigeria dadai sauran masana harkar Kudi dake fadin Kasarnan, kuma Taron yagudanane cikin Natsuwa da Kwanciyar Hankali daga farkon Taron har zuwa karshe,

Hakanne yasa yazamo dole a yabawa wanda ya Jagoranci wannan Taron wato Alh Dr. UMARU KWAIRANGA Sarkin Fulanin Gombe domin irin Namijin Kokarin dayayi wajen ganin Taron anfara Lafiya angama Lafiya. Muna Addu'a ALLAH yakaramar Basira, yakaramar Kwazo da Kwarin Guiwa ya karamar Girma da Daukaka a Fadin Duniya

Comments

Popular posts from this blog

WHO IS ALH (DR) UMARU KWAIRANGA (SARKIN FULANIN GOMBE)

Tarihin Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa

WAYE SARKIN FULANIN GOMBE